CryptoNews

Yadda Ake Samun Good Mentor A Web3 Da Cin Moriyar Mentorship

A Wannan Article Din Zaka Koyi Yadda Ake Samun Good Mentor A Web3 Da Cin Moriyar Mentorship, Sannan Wannan Article Zata Taimakawa Mai Karantawa Wajen Sanin Mahimmancin MENTOR A Crypto Dama Web3 Gaba Daya.

 

Yadda Ake Samun Mai Ba Da Shawara (Mentor) da Muhimmancin Shi

 

Yadda mutane suke kukan rashin “mentorship”, ba wai rasa shi suka yi ba, a’a ina ganin ba su san yadda ake cin moriyarsa ba ne.

Mentor” shi ne wanda ka rike a matsayin maigida, wanda zai rinka ba ka shawarwari, idan ka yi abu ba daidai ba ya nuna maka, ya yi guiding dinka, da sauransu.

Amma ga wasu matakai a takaice idan kana son samun mentor da cin moriyar mentorship kamar haka:

1 — Mentors sun rabu kashi-kashi kamar haka: wani mentor din a bangaren koyon skills ko kasuwanci ne, wani a bangaren sha’anin rayuwa ne. Wanda ya kamata ka fara zaba shi ne na sha’anin rayuwa. Inda ya kamata ka same shi shi ne malaminka na makaranta, maigidanka na wajen a aiki, senior dinka, wani lokaci ma abokinka ne. Idan malaminka ne ko maigidanka, ka tambaye shi, “Malam/Sir, wadanne abubuwa ne wadanda ya kamata a ce na daina, ko kuma a matsayinmu na matasa…. Mal/Sir/Oga, wadanne shawarwari za ka ba ni a matsayina na yaronka/dalibinka….” Duk ingantacciyar shawarar da aka ba ka kada ka raina ta.

2 — Mentor na harkokin kasuwanci ko skills, shi ne maigidanka wanda za ka rinka binsa sau-da-kafa. Duk abun da ya yi wanda ba ka gane ba ka tambaye shi cikin ladabi. Yawancin abubuwan da za ka yi ka rinka tuntubarsa, “Sir, na kammala wannan, wanne next step ya kamata na dauka? Oga wanne abu ne kake ganin ya dace a nan?”

3 — Ba a yin mentor daya, za ka iya tara sama da biyar, saboda kowanne akwai inda yake shaping din rayuwarka. Duk wanda ka ga yana da wani ilimi ko kwarewa wacce za ka bukata, ka manne masa. Ka yi kokari duk lokacin da kake tare da su ko kake sauraronsu ya kasance ka koyi wasu muhimman abubuwa a wajensu. Musamman malamai, kusan duk abun da za su fada maka ilimi ne mai tsada.

KURAN-KURAN DA MUKE YI A NEMAN MENTORSHIP

1 — Rashin girmama mentor: matasa da dama (wadanda suke shiyyarmu ta Gen-Z) ba su iya magana ba ballantana girmama mutum. Haka muke gantsaro magana gatse-gatse mu dannawa wani mutum mai ilimi da sunan neman mentorship, idan kuma ya share don kare martabarsa sai mu zage shi. Wannan babban kuskure ne. Mu muke nema a wajensu, dole za mu ba su girmansu. Cikin littafin V., ya ce “Babu ruwanka wai yaya aka yi maigidanka ya samu girma ko batun cancantarsa. Kawai ka girmama shi.”

2 — Rashin hakuri: mu da muke nema, mu ya kamata mu yi hakuri. Wani idan ya kira mentor a waya ya ji bai daga ba, ba ya tunanin wani uzuri yake yi, sai ya dame shi da kira. Bugu da kari, ba a yi wa mentor voice note ko video call. Kar ka kira shi sai ya ba ka time. Kar ka kira shi a lokacin da bai dace ba. Kar ka kira shi idan kana cikin hayaniya.

3 — Takura: babu wani mentor da yake son takura. Yawancin Gen-Z kuma akwai takura, sun dauka mentorship ma kamar soyayya ce ko hawa TikTok. To ba haka yake ba. Kar ka takura masa, idan kuma ka yi, to hakika zai daina kula ka. Sannan the most important, ba dole sai ka yi magana da shi ba!

4 — Rashin sanin darajar ilimi: watakila wannan shi ya kamata ya zama na farko ma. Ba mu san irin kalubalen da mentor ya sha lokacin karatu ba, da irin gwagwarmayar da ya tsallake, da irin fadi-tashi da ya yi da sauransu. Wasu kawai burinsu shi ne duk lokacin da suka bukaci attention dinsa, to ya bar duk abun da yake yi (ko sallah yake yi ko yana tare da iyalinsa) ya rugo ya amsa kiransu, ya yi solving problems dinsu sannan ya samu zaman lafiya.

5 — Rashin sanin girman mentorship: kamar dai yadda na fada a sama, wasu gani suke wajibi ne mutum ya zama mentor dinsu. To ba dole ba ne. Sai ya ga dama, saboda babu wanda ya wajabta masa. Dole za mu san cewa kasancewarsa mentor dinmu alfarma ya mana. Dole za mu san girman mentorship din.

Wadannan su ne abubuwan da nake ganin ya dace mu yi don neman mentorship.

Game da koyar da #digitalSkills da muke yi a Flowdiary kowanne course akwai mentor dinsa. Mentor zai ba ka lokaci ya yi guiding dinka. Muna da tsarin FREE MENTORSHIP kuma. Ina fatan za mu kiyaye abubuwan da na lissafo a sama.

Kuma ba a nan kadai ba ne, duk inda kake a duniya matukar za ka kiyaye wadannan abubuwan, ina mai tabbatar maka cewa za ka ci moriyar mentorship insha Allahu.

—Muhammad Auwal Ahmad (#Mohiddeen)
CEO, Flowdiary

17th December 2024

Flowdiary Team
Flowdiary Team

Flowdiary makarantar yanar gizo ce da ke koyar da digital skills kala-kala da harshen Hausa ga dubunnan matasa don su yi amfani da su wajen dogaro-da-kai.

A Flowdiary Suna koyar da kwasa-kwasan na’ura da yanar gizo kala-kala irin su Android App Development, Full Stack Web Development, Smartphone Graphic Design, Digital Marketing Mastery, Professional Bug Hunting, Smartphone Video Editing, Social Media Marketing da sauransu cikin sauki.

Flowdiary Core Values

    • Koyar da digital skills a harshen Hausa saboda a fahimta sosai, kamar yadda Turawa, Chinese, Indians, Arabs, da Turkish suke yin nasu —putting an end to language barrier by teaching the most in-demand digital skills in Hausa Language with our world-class courses.

 

    • Samar da jagoranci wanda zai nuna wa dalibai abubuwa daki-daki don cimma kudirin gina kai a duniyar fasaha —providing excellent one-on-one mentorship and required tools to help youth build careers in the tech industry, regardless of their background.

 

  • Karfafa dogaro-da-kai da ilimin na’ura don rage rashin aikin-yi da bude wa matasa damammakin ayyuka —enhancing education for self-reliance to reduce the high rate of unemployment by flowing job oppurtunities to our students through internships and guidance to strive in the international tech market.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button